1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-Moon ya ce ana aikata mummunan kisa a Siriya

March 3, 2012

Yayin da sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon yace gwamnatin Siriya na aikata ta'asar kisan jama'a a waje guda jakadan Siriyan yace ƙazafi ake yiwa ƙasarsa.

https://p.dw.com/p/14EMD
epa03088377 UN Secretary-General Ban Ki-moon speaks during a joint press conference with the Palestinian Authorities President Mahmoud Abbas (unseen) in the West Bank town of Ramallah on 01 February 2012. UN Secretary-General Ban Ki-Moon kicked off a series of meetings 01 February with Israeli and Palestinian leaders, holding talks in Jerusalem with President Shimon Peres. EPA/ATEF SAFADI
Ban Ki-MoonHoto: picture-alliance/dpa

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya buƙaci gwamnatin Siriya ta shugaba Bashar al-Assad ta baiwa jami'an agaji damar shiga birnin Homs domin kai taimakon jin ƙai, ya na mai baiyana takaici cewa majalisar Ɗinkin Duniyar ta sami rahotannin aikata ta'asar kisan kai da kuma azzabatar da al'umma. "Mun ga yadda ake luguden wuta da mayan tankokin yaƙi a unguwanni dake cunkushe da jama a faɗin ƙasar musamman kuma a birnin Homs. Yace Majalisar Ɗinkin Duniyar ta sami rahotanni ana aikata ta'asar kisan kai da kuma azzabatarwa akan jama'a fararen hula"

Jakadan Siriya a Majalisar Ɗinkin Duniya Bashar Ja'afari ya zargi Ban Ki-Moon da yiwa Siriya ƙazafi yana mai baiyana 'yan adawa da cewa 'yan ƙungiyoyin ne na ta'adda waɗanda kuma ke ɗauke da makamai. Ban Ki-Moon yace ba da jimawa sabon manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen larabawa Kofi Annan zai kai ziyara ƙasar ta Siriya.

A waje guda dai ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce hukumomin Siriya sun cigaba da datse hanyoyin kai kayan agaji zuwa Baba Amr dake yammacin birnin Homs. Shi ma wani ɗan jaridar ɗaukar hoto na Birtaniya Paul Conroy wanda ya kuɓuta daga birnin na Homs da 'yan raunuka ya baiyana halin da ake ciki da cewa yanayi ne na kisan kan mai uwa da wabi akan magidanta maza da mata da kuma yara ƙanana.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh