1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bama za ta sake fursunoni 651 a wannan juma'ar

January 13, 2012

Daga cikin furzunoni da gwamnatin Bama za ta yafe musu laifuffukan da suka aikata har da fursunan siyasa ɗaya. A jimilce dai mutane 27 000 gwamnati ta sake tun bayan mayar da mulki ga hannun farar hula a Bama.

https://p.dw.com/p/13j74
Myanmar pro-democracy leader Aung San Suu Kyi delivers a speech as she meets young members at the headquarters of the National League for Democracy on Tuesday, Dec. 28, 2010, in Yangon, Myanmar. (AP Photo/Khin Maung Win)
Aung San Suu Kyi ta yaba matakin sako fursunoni a ƙasar Bama.Hoto: AP

Sabbin hukumomin Myanmar ko kuma Bama na shirin sako Min Ko Naing, wato ɗaya daga cikin fitattun fursunan siyasa na wannan ƙasa. Wannann mataki na su na ƙunshe ne cikin shirin gwamnatin na sako furzunoni 650 a wannan juma'ar bayan an yafe musu laifukan da suka aikata. Gwamnatin mulkin demokardiya ta bama mai ci a yanzu wadda kuma ke da goyon bayan sojoji, ta sallami ɗaurarun 27 000 tun bayan da ta kama aiki a watan mayun bara. sai dai ƙalilan daga cikin waɗanda aka sake ne fursononin siyasa.

Wannan mataki ya zo ne kwana ɗaya bayan da gwamnati ta rattaɓa hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen ƙabilar Karen bayan shekaru 60 ana kai ruwa rana tsakaninsu. Tun dai 1949, wato shekara ɗaya bayan samun 'yancin kan bama daga turawan mulkin mallaka na Ingila ne, mayaƙan sa kai na Karen suke neman a sakar wa yankinsu marar gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba ter da tsangwama ba. A lokacin gwamnatocin mulkin soja na bama dai, an ta zargan dakaru gwamnati da tasa ƙeyae wasu 'yan ƙabilar Karen daga garuruwwansu i zuwa wasu sansanoni da ke kan iyakar ƙasart a Bama da kuma Thailand.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi