1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Bakin haure da dama sun mutu a cikin ruwan Faransa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 15, 2024

Bakin hauren sun fito ne daga kasashen Eritrea da Sudan da Syria, sai Afghanistan da Masar da kuma Iran

https://p.dw.com/p/4kdzK
Hoto: Denis Charlet/AFP

Kimanin mutane takwas ne suka rasa rayukansu a cikin ruwan yankin arewacin Faransa, yayin kokarinsu na tsallakawa zuwa Birtaniya kamar yadda ma'aikatar kula da gabar ruwan Faransa ta sanar a Lahadin nan.

Karin bayani:Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya

Hukumomin kasar sun ce lamarin lamarin ya faru ne cikin daren Asabar, inda suka hango kwale-kwale dauke da tarin mutane duk a jigace.

Karin bayani:Dubban bakin hauren na nuna bukatar komawa gida

Daga nan ne suka aike da jirgi mai dauke da jami'an agaji, kuma nan da nan suka kubutar da bakin haure 53 tare da ba su kulawar gaggawa cikinsu har da jariri 'dan watanni 10 da ke fama da sanyi.

To sai dai duk da hanzarin da suka yi ba su samu nasarar ceto rayukan mutane takwas din ba, wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Bakin hauren sun fito ne daga kasashen Eritrea da Sudan da Syria, sai Afghanistan da Masar da kuma Iran.