1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin ruwa ya kife da mutane 43

Abdul-raheem Hassan LMJ
July 3, 2021

Wani jirgin ruwa makare da bakin haure ya kife a ruwa, a kokarin da suke na tsallaka wa Tekun Bahar Rum daga Libiya zuwa Italiya. Sai dai jami'an agaji a gabar ruwana Tunisiya sun ceto mutane 84.

https://p.dw.com/p/3vyfJ
2020 mehr Menschen denn je auf der Flucht
Hoto: Bruno Thevenin/AP/dpa/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa, yawancin wadanda ke cikin jirgin sun fito ne daga kasashen Masar da Sudan da Iritriya da kuma Bangaladesh duk a kokarin neman mafita da rayuwa mai inganci a kasashen Turai.  Yake-yake da wasu matsaloli da ake fama a wasu kasashe, na taka rwa wwajen tilasta bakin hauren yin kaura.

Alkaluman gwamnatin Italiya ya nunar da cewa kusan bakin haure dubu 20 ne suka yi nasarar tsallakawa Tekun Bahar Rum, daga farkon wannan shekara ta 2021 zuwa watan Yuli da muke ciki.