1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu wanda ya tsira da rai a hadarin jirgin sama a Brazil

August 10, 2024

Rahotanni daga Brazil sun yi nuni da cewa, wani jirgin sama mai dauke da mutane kimanin 61 ya yi hatsari a jihar Sao Paulo.

https://p.dw.com/p/4jJmr
Jami'an 'yansandan Brazil a wurin da hatsarin jirgin sama ya auku
Jami'an 'yansandan Brazil a wurin da hatsarin jirgin sama ya aukuHoto: Andre Penner/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil da sauran jami'an kasar sun yi hasashen cewa ta yiwu dukannin fasinjojin da kuma ma'aikatan jirgin da hadarin ya rutsa da su sun rigamu gidan gaskiya. Faya-fayan bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jirgin kamfanin Voepass Linhas Areas, ya rikito daga sama zuwa kan wasu rukunin wasu gidaje.

Karin bayani: Hadarin jirgin sama a Brazil

Jami'an kwana-kwana da kuma ma'aikatan agaji na gudanar da aikin ceto yayin da wasu jami'an suka ce sun gano na'urar bayanai ta cikin jirgi wato black box a turance. Gwamnatin Jihar Sao Paulo ta mika jajjenta tare da goyon baya ga iyalan wadanda da hatsarin ya rutsa da su.