1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP25: An gaza cimma matsaya a taron sauyin yanayi

Abdourahamane Hassane
December 14, 2019

Wakilai na kasashe 200 da ke halartar taron kare muhali na COP25 na Majalisar Dinkin Dinkin a birnin Madrid na kasar Spain sun gaza cimma matsaya kan rage yawan hayakin mai illa da ake fiddawa a duniya.

https://p.dw.com/p/3Unoa
Spanien COP 25. UN-Klimakonferenz in Madrid
Hoto: picture alliance/AP Photo

Taron wanda ya kamata a kammala ranar Juma'a an tsawaitashi har ya zuwa ranar Asabar (14.12.19) saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin kasashen wajen rage hayaki mai illa ga muhali da maki biyu kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a Paris a shekara  ta 2015 ta tanada.

Kasashen China da Indiya da Japan da Amirka da ke kan gaba wajen fitar da hayakin mai guba ba su kai ga amincewa da dokokin da taron ya tattauna a tsawon makonnin biyun a aka share ana gudanr da shi a birnin Madrid na kasar Spain ba.