1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar rana ga al'ummar kudancin Sudan

January 7, 2011

Kwararar yan Kudancin Sudan zuwa gida domin shiga zaben raba gardama a karshen mako, da halin da ake ciki a kokarin sulhunta rikicin Cote d'Ivoire sune suka dauki hankali a wannan mako.

https://p.dw.com/p/zuk3
Tutar mulkin kan Kudancin SudanHoto: DW

Al'amura ukku ne muhimimai daga cikin wadanda jaridun na Jamus a wannan mako suka fi maida hankali kansu a sharhunan da suka shafi nahiyar Afrika. Abu na farko shine halin da ake ciki na kiki-kaka a kasar Cote d'Ivoire, inda Laurent Gbagbo yaki sauka daga mukamin shugaban kasa, duk kuwa da kayar dashi da Alassane Ouattara yayi a zabe na biyu cikin watan Nuwamba. Jaridun sun kuma duba zaben raba gardama a game da makomar kudancin Sudan, inda wasu ma suka yi sharhin cewra idan mazauna yankin suka zabi ballewa, ko dai kudanci da arerwaci su yi zaman makwabtaka na gari, su ci ribar juna, ko kuma su sake fadawa yaki tsakanin su, sai kuma kasar Kenya, inda manyan ministoci sukai ta murabus, domin su kaucewa zargin cin rashawa da ya zama ruwan dare a wannan kasa.

A game da halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire, inda shugaban kasa dake kan gado, Laurent Gbagbo yaki mika mukamin ga hannun zababben shugaba, Alassane Ouattara, jaridar Frankfurter Allgeieine Zeitung ta fara sharhin ta ne da tambayar, shin wanene zai kori wani a kasar ta Cote d'Ivoire. Duk da kokarin shugabanin kasashe makwabtaka da kungiyar kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS da kungiyayr AU, amma Gbagbo yace ba zai sauka ba daga mukamin shugabancin kasar ba, yayin da majalisar dinkin duniya tayi gargadi a game da yakin basasa da samun kisan kare dangi. Jaridar tace tuni manyan kasashen duniya suka juyawa Gbagbo baya, suka kuma umurci al'umar su dake Cote d'Ivoire su janye, amma hakan bai hana shugaban mai ci kafewa kan kujerar sa ba. Abin da kadai yace zai yi shine ya gana da abokin takarar sa Ouattara.

Elfenbeinküste / Koroma / Gbagbo
Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma (hagu) bayan ganawa da Laurent GbagboHoto: AP

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta duba halin da ake ciki ne a Cote d'Ivoire, inda tace wakilan kungiyar AU da na ECOWAS hakar su dai har yanzu bata cimma ruwa ba, a kokarin samun sulhunta rikicin siyasa na wannan kasa. Jaridar tace shugabannin kasashen Benin da Saliyo da Cape Verde da Pirayim ministan Kenya duk sun kare tattaunawar su a Abidjan a farkon mako ne ba tare da sun ja hankalin Laurent Gbagbo, da ya sha kaye a zaben shugaban kasar a karshen watan Nuwamba ya sauka, ya mika wannan ofishi ga wanda duniya gaba daya ta yarda cewar shine ya lashe zaben, wato Alassane Ouattara ba. Amerika da kasashen Afrika da dama sun yi wa Gbagbo tayi mafakar siyasa amma har yanzu yaki mika kai bori ya hau. Jaridar Berliner Zeitung tace ya zuwa yanzu mutane fiye da 200 ne suka mutu a kasar ta Cote d'Ivoire babu gaira babu dalili.

Ranar Lahadi za'a gudanar da zaben raba gardama a yankin kudancin Sudan, inda mazauna yankin zasu yanke kudiri a game da ko suna bukatar ci gaba da zama a taraiyar Sudan ko kuma zasu kasance masu cikakken yancin kansu. Jaridar Handelsblatt tayi hangen abin da zai zama sakamakon wannan zabe na raba gardama, inda tace Sudan ta kama hanyar darewa gida biyu. Wannan zabe wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekara ta 2005, wadda ta kawo karshen yakin basasa na tsawon fiye da shekaru 20 a yankin. Sudan, da tafi yawa girman fadin kasa a Afirka, tana hako man fetur fiye da ganga dubu 500 ne a kullum, inda fiye da kashio 90 cikin dari na wannan adadi yake fitowa daga kudancin ta.

Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi kan makomar yankin na kudancin Sudan da cewar ga mazauna wannan yanki, ranar ta Lahadi, muhimmiyar rana ce ga rayuwar su. Tace idan har suka zabi samun yancin su, zasu rayu ne a wata kasa dake cikin wadanda suka fi rashin ci gaba a duniya. To sai dai jaridar tace akalla zasu rayu cikin yanci, bayan da suka yi zargin cewar shekara da shekaru gwamnatin tsakiya a Khartoum tana maida su saniyar ware.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Halimatu Abbas