Babban taron duniya a birnin Paris kan makomar Libiya
September 1, 2011Jami'ar kula da harkokin wajen EU Catherine Ashton wadda ta ba da sanarwar ɗage takunkuman a birnin Brussels ta ce an janye haramci da aka sanya wa kamfanonin da hukumomin Libiya guda 28, ciki har da bankuna da kamfanonin mai da na isakar gas. A Jamus kaɗai an ƙiyasta cewa kadarorin Libiya dake cikin ƙasar sun kai na Euro miliyan dubu 7.3, a saboda haka ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira da a gaggauta sakin waɗannan kuɗaɗe domin taimakawa al'umomin Libiya.
"Libiya ƙasa ce mai ɗinbim arziki da ya wuce misali musamman na makamashi. Saboda haka ya kamata a ɗage wannan takunkumin da aka ɗaro wa gwamnatin Gaddafi, domin taimakawa a fannonin kiwon lafiya da samar da abinci da sake gina wasu ɓangarorin ƙasar da aka lalata."
Sa'o'i ƙalilan gabanin buɗe babban taron duniya kan ƙasar ta Libiya a birnin Paris na ƙasar Faransa, Rasha mai ikon hawa kujerar naƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da majalisar wucin gadin 'yan tawayen Libiya a matsayin halastacciyar wakiliyar ƙasar.
Shugaban Faransa wanda ya kira taron na Paris a wannan Alhamis, ya jaddada rawar da ƙasarsa da kuma Birtaniya suka taka a matakan sojin da ƙungiyar NATO ta ɗauka kan Libiya.
"A karon farko tun bayan shekarar 1949, NATO ta tafiyar da aiki a matsayin wata ƙungiyar ƙawance wadda ƙasashen Turai guda biyu wato Birtaniya da Faransa suka jagoranta."
Shugaban na Faransa ya jawo hankali cewa tun farko Amirka ba ta yi niyar shiga a dama da ita sosai a Libiya ba.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu