1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pekin: Kasashen Afrika za su tattauna tare da Chaina

Salissou Boukari
September 3, 2018

A wannan din ce Litinin aka soma babban zaman tsakanin Chaina da Afirka a birnin Beijing na kasar ta Chaina, taron ya samu halartar shugabanni da dama na kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/34CKD
Ruanda Besuch Xi Kinping Paul Kagame
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Tsawon kwanaki biyu ne dai shugabannin na Afirka tare da shugaban kasar ta China Xi Jinping za su shafe suna tattauna batutuwa daban-daban cikinsu har da sake duba dokokin yarjeniyoyin da suke kullawa da kasar ta Chaina.

Wannan taro kuma zai samu halartar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres, inda ake kallon taron a matsyin wata kasaitaciyar haduwa ta diflomasiyya wanda zata tattara kimanin mutane miliyan daya.

Shugaban kasar Cote d'Ivoir Alassane Dramane Ouattara ne dai ya fara isa kasar ta Sin tun daga ranar 28 ga wata, kafin shugaban kasar Benin Parice Talon da na Senegal Macky Sall su take take masa baya. Akwai kuma sauran shugabannin irin su Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya da Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar da za su halarci wannan babban zaman taro.

Kasar Maroko dai ta samu wakilci daga firaministanta, yayin da Algeriya ta aike da ministan harkokin wajenta wurin wannan taro. Kasar Swaziland ce kadai ba za ta halarci wannan taro ba, ganin har yanzu ta na da hulda da kasar Taiwan.