1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban sakataren MƊD yayi kira da a kawo ƙarshen tashe tashen hankula a Siriya

August 7, 2011

Ban Ki Moon ya tattauna da shugaban Siriya Bashar Al-Assad ta wayar tarho inda ya nuna masa damuwar gamar ƙasa da ƙasa.

https://p.dw.com/p/12CRg
Mahukuntan Siriya na ci-gaba da ɗaukar matakan ƙarfi akan masu zanga-zangaHoto: AP Photo / SHAMSNN

Babban sakataren Majalisa Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kira ga shugaban Siriya Bashar al-Assad da ya kawo ƙarshen matakan ƙarfi da yake ɗaukan akan fararen hula nan-take. Kamar yadda majalisar a birnin New York ta nunar, a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, Mista Ban ya nuna wa Assad matuƙar damuwar gamaiyar ƙasa da ƙasa game da matakan murƙushe 'yan adawa masu zanga-zanga da gwamnatinsa ke yi. Shi ma Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya soki lamirin Siriya da kakkausan lafazi, yana mai cewa haƙurin ƙasarsa ya ƙare game da gwamnatin Assad. Erdogan ya ce a ranar Talata mai zuwa ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu zai kai ziyara Siriya domin miƙa saƙon Turkiya ga mahukuntan Siriya. Da farko su ma ƙasashen Larabawa na yankin Golf sun yi kira da a kawo ƙarshen matakan ƙarfin da ake ɗauka kan masu adawa da gwamnati. Mai kula da batutuwan cin zarafin bil Adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Christof Heyns ya ce gwamnatin Siriya tana fatali da 'yancin yin gangami:

"Haƙƙin gwamnati ne ba da izinin 'yancin faɗin albarkacin baki da yin taruka, amma a wannan ƙasa sojoji na amfani da tsinin bindiga akan mutane da su da makami. Wannan mummunan keta 'yancin rayuwar jama'ar da abin ya shafa ne."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal