1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD tana neman sasanta Putin da Zelensky

Suleiman Babayo MAB
April 20, 2022

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci ganawa da shugabannin kasashen Rasha da Ukraine, domin sasanta yakin da ke faruwa.

https://p.dw.com/p/4AAMf
Ukraine-Krieg | UN-Sicherheitsrat | Antonio Guterres
Hoto: Andrew Kelly/REUTERS

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci ganawa da shugabannin kasashen Rasha da Ukraine. Mai magana da yawun majalisar ya ce babban jami'in zai gana da kowane shugaba a kasarsa. Tuni Guterres ya tura wasikar neman ganawar ga Shugaba Vladimir Putin na Rasha da kuma Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine.

Wannan na zuwa lokacin da mahukuntan birnin Moscow na Rasha suka yi ikirarin tura bukatar neman sasanta rikici ga kasar ta Ukraine. Mai magana da yawun fadar mulkin Rasha bai tantance abin da takardar ta kunsa ba.

Rasha tana kara azama a kutsen da ta kaddamar a kan kasar ta Ukraine. Dubban sojojin kasar ta Rasha suna ci gaba da kutsawa yankin Danbas na gabashin Ukraine da ya bayyana ballewa, kuma yake dauke da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.