1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Auren Yarima William

April 29, 2011

An ɗaura auren Yarima William na Birtaniya da Kate Middleton a ginin cocin Westminster Abbey da ke birnin London

https://p.dw.com/p/116ai
William da Kate tsaye bayan ɗaurin aurensu a wajen ginin Westminster AbbeyHoto: dapd

Da safiyar ranar 29 ga watan Afrilu limamin cocin Ingila, Achbishop of Canterbury ya ɗaura auren Yarima William na Birtaniya da Kate Middleton a ginin cocin Westminster Abbey da ke birnin London. Mutane 2000 cikinsu har da waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban irinsu mawaƙin nan Elton John da ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan David Beckham aka gayyata zuwa bukin ɗaurin auren. An kuma samu mutane miliyan dubu biyu da suka hallara domin ganin yadda bukin zai gudana.

Kate und William Hochzeit 29.04.2011
William da Kate cikin keken doki kan hanyar zuwa fadar BuckinghamHoto: AP

Ko kafin a shiga wannan buki sai da kakar yariman, Sarauniya Elizabeth ta naɗa ma jikan nata rawani a matsayin magajin garin Cambridge inda hakan ya sanya ita kuma amaryar tasa, Kate Middleton a matsayin magajiyar wannan gari kai tsaye. Bayan ɗaurin auren ne kuma a karon farko Yarima William da amaryarsa Kate Middleton suka bayyana a gaban jama'a suka kuma sumbancin juna a matsayinsu na ma'aurata a fadar Buckingham.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu