1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi auren daya daga cikin masu jiran gadon sarautar Ingila

May 19, 2018

An yi auren Yarima Harry daya daga cikin masu jiran gadon sarautar Ingila da amaryarsa Gimbiya Meghan.

https://p.dw.com/p/2xzpS
UK | Hochzeit Prinz Harry & Meghan Markle |
Hoto: Reuters/D. Sagolj

An daura auren Yarima Harry na gidan sarautar Ingila da amaryarsa Meghan wadda ta zama gimbiya bayan daura auren a cocin Windsor. Shi dai Yarima Harry ya kasance yanzu haka mutum na shida cikin jerim masu jiran gadon sarautar Ingila daga hannun kakarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Dubban mutane suka halarci dauren aure kana wasu milyoyi suka kalla ta tashoshin talabijin a bangarori daban-daban na duniya.

Ana sa ran bikin auren ya janyo wa kasar ta Birtaniya ta samu kudaden shiga daga euro milyan 50 zuwa kusan mulyan 100 da wasu milyanyoyin na kayayyakin da ake hada-hada albarkacin auren. Kuma kowace shekara Birtaniya tana samun makuden kudaden shiga saboda masarautar da kayayyakin tarihi da ta kunsa galibi daga masu yawon bude ido.