1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta yi kira da a tsagaita buɗe wuta a Libiya

June 16, 2011

Ƙungiyar Gamayyar Afirka (AU) ta soki Majalisar Ɗinkin Duniya akan matakin soji da take ɗauka akan Shugaba Mumammar Gaddafi na Libiya

https://p.dw.com/p/11bZ3
Jacob Zuma, mai magana da yawon AU akan LibiyaHoto: picture-alliance/ dpa

Ƙungiyar Gamayyar Afirka (AU) ta yi gargaɗi game da haɗarin da ke tattare da matakin soji da Majalisar Ɗinkin Duniya ke ɗauka akan Libiya. Ministocin Afirka su yi kira da a dakatar da ɗaukar wannan mataki domin a samu damar ci gaba da bin hanoyon siyasa domin magance rikicin na Libiya. Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATo ta fara kai hare hare akan ƙasar ta Libiya ne bayan da komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsai da ƙudurin zaratar da dokar hana tashin jiragen sama a wannan ƙasa da nufin kare farar hula. Shugaba Jacob Zumah na Afirka ta Kudu wanda ɗaya ne daga cikin masu sukan Majalisar Ɗinkin Duniya game da wannan mataki nata yace luguden wuta da ake yi akan Shugaba Muammar Gaddafi ya wuce gona da iri .

A dai halin yanzu wakilin Birtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga shugabannin Afirka da su yi kira ga Gaddafi da ya sauka daga karagar mulki. An gudanar da taro akan Libiya a birnin New York ne bayan da babban sakataren NATO, Anders Fogh Rasmussen ya kai ziyara a birnin London inda ya shawarta aikin da Ƙungiyar NATO ke yi a Libiya tare da Fraiminista David Cameron da sakataren harkokin waje William Hague.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita Umaru Aliyu