1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta dakatar da Gabon daga ayyukanta

August 31, 2023

Majalisar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar Tarayyar Afirka AU ta sanar da dakatar da kasar Gabon daga dukannin ayyukanta sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi.

https://p.dw.com/p/4Vp0T
Shugaban rikon kwarya a Gabon, Janar Brice Oligui Nguema
Hoto: AFP/Getty Images

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban gwamnatin soji ta rikon kwarya. A cewar jagororin da suka yi juyin mulki a kasar, Oligui zai jagoranci Gabon nan da zuwa wani lokaci, ko da yake ba su bayyana tsawon lokacin da za su rike madafun ikon kasar ba kafin mayar da ita kan tafarkin dimokradiyya.

Karin bayani: Sharhi: Nazari a game da yunkurin juyin mulkin Gabon

Kakakin kwamittion rikon kwarya, Ulrich Manfoumbi Manfoumbi ya bukaci dukannin sakatarori da ministoci da daractoci da sauran jami'an gwamnati da su koma bakin tare da ci gaba da gudanar da ayyukan jama'a.

Ya kuma kara da cewa, Janar Oligui ya na mai tabbatarwa dukannin abokan huldar kasar cewa, zai dauki dukkanin matakin da ya kamata wajen kare mutuncin kasar a cikin gida da kuma ketare.