Atisayen sojin Rasha da China
April 23, 2012Ƙasashen China da Rasha sun fara atisayen haɗin gwiwa na sojojin ruwan su a wannan Lahadin. A cewar kanfanin dillancin labaran ƙasar China, atisayen, wanda ke zama irin sa na farko, za'a ɗauki tsawon kwanaki shidda ne ana yin sa akan tekun dake gabashin China na Yellow Sea. China ta tura manyan jiragen ruwan ɗaukar ƙananan jiragen saman yaƙi guda biyu, kana da manyan jiragen ruwa 16 da kuma fiye da sojoji dubu huɗu, a yayin da Rasha kuma manyan jiragen ruwa bakwai da suka haɗa da waɗanda ke lalata makamai masu lnzami. Atisayen soji na ƙarshen da ƙasashen biyu suka yi haɗin gwiwar yin sa dai ya kasance a shekara ta 2005 ne, amma kuma wannan shi ne atisaye na farkon daya shafi mayaƙan ruwa, kamar yanda wani ƙwararre a ƙasar China ya sanar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas