1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku ya zabi mataimaki a yankin Igbo

Yusuf Bala Nayaya
October 13, 2018

Babbban dan takarar adawa ga Shugaba Muhammdu Buhari na Najeriya ya zabi wanda zai zama mataimakinsa wanda ke zama tsohon gwamna daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya kamar yadda mai magana da yawun Atiku ya bayyana.

https://p.dw.com/p/36TdY
Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya da zai yi takarar shugabancin kasar a watan Fabirairu shekarar 2019 karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya zabi Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya don kalubalantar Shugaba Buhari.

Wannan zabi dai ana kallonsa a matsayin wata dabara ta mamayar yankin na Kudu maso Gabashin Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ke da rauni a zaben da ya gabata. Yayin da kuma ake fuskantar kalubale daga wannan yanki saboda masu rajin ballewa da ke son kafa kasar Biafra, wadanda yunkurinsu ya sanya gwamnati tura dakarun tsaro yankin don dakile kokarin na 'yan awaren Biafra.