1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asusun tallafa wa Palasdinawa

Usman Shehu Usman
April 17, 2024

MDD ta kaddamar da asusun neman kudi kusan dala biliyan uku, don tallafa wa yankin Gaza MDD na son samun kudin ne don samar da abinci wa al'ummar Palasdinawa da ke a Gaza da yammacin kogin Jordan.

https://p.dw.com/p/4etF7
Gazastreifen I Humanitäre Lage in Rafah
Hoto: Mohammed Salem/REUTERS

Neman agajin wanda a wannan Laraba hukumar kula da ayyukan bayar da agajin gaggawa ta MDD da aka sani da OCHA, tac e tallafin ana son ceto Palasdinawa sama da miliyan uku daga bala'in yunwa, kan nan da karshen bana. Daga kudin MDD ta ce za a ware dala miliyan 782 kan sayan abinci ga al'ummar Gaza sama da miliyan biyu da yanzu ke matukar fiskatar hatsarin rayuwa bisa karancin abinci, haka kuma ta yi kiyasin akwai wasu Palasdinawa dubu 400 a yammacin kogin Jordan, da ke matukar neman tallafin abinci. Yakin sama da watanni shida da yankin na Palastinawa ke fiskanta ya haddasa tamuwa a yankin Gaza musamman don karancin abinci a cewar MDD.