1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asusun IMF zai agaza wa kasar Masar

Usman ShehuJanuary 8, 2013

Asusun bada lamuni na duniya wato IMF, ya tura jami'ai a kasar Masar don tattauna matsalar tattalin arzikin kasar.

https://p.dw.com/p/17Fu8
Egyptian President Mohamed Morsi speaks to his supporters outside the presidential palace al-Ethadeya, where tens of thousands of Egyptians rally to support Morsi's new constitutional declaration issued in Cairo, Egypt, on November 23, 2012
Shugaban kasar Masar Mohamed MursiHoto: picture-alliance/dpa

Jami'an Asusun bayar da lamuni a duniya na IMF isa birnin Alkahira na kasar Masar domin tattauna yiwuwar tallafawa kasar ta farfado da tattalin arzikinta. Masood Ahmed, darekta a asusun dake kula da sashen yankin Gabas Ta Tsakiya da kuma Asiya, ya ce a wannan Litinin ya gudanar da tattaunawa mai amfanin gaske tare da shugaba Mohammed Mursi na Masar da kuma manyan jami'an gwamnatin kasar akan kalubalen da tattalin arzikin kasar ta Masar ke fuskanta. Ya ce a lokacin tattaunawar ce suka amince da aiwatar da tsare-tsaren inganta sashen bunkasa kananan masana'antu da kuma daukar matakan shawo kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fama da shi a baya bayannan.

A wani labarin da ya shafi kasar Masar: Akalla yan sanda biyu suka mutu a wani musayar wuta tsakanin jami'an staro da yan bindiga a kudancin kasar. Babban jami'in yan sanda a jihar da lamarin ya faru, yace fada ta barke bayan da yan sanda suka nemi tarwatsa kungun yan fashi da suka addabi yakin. Yan fashin dai sun tsere daga motar yan sanda amma daga bisani an kamo dayansu. Kasar Masar na fama da matsalolin tsaro, tun bayan sauyin gwamnati da aka samu a kasar biyo juyin juya hali da ya kifar da gwamnatin Husni Mubarak.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamadou Awal