1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Assimi Goïta ya ba wa gwamnati umarnin shirya zabe a Mali

December 3, 2024

Ba zato ba tsammani ne gwamnatin Mali ta bayyana shirin gudanar da zabe da zai kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru. Sabon firaminista Janar Abdoulaye Maiga ne aka ba wa umurnin shirya wannan zabe cikin tsanaki.

https://p.dw.com/p/4ngeR
Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita ya sha alwashin shirya zabe cikin tsanaki
Shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita ya sha alwashin shirya zabe cikin tsananiHoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

 Wannan yunkuri ya kasance guda daga cikin abubuwan da ajandar sabuwar majalisar ministocin da aka kafa a baya-bayan nan ta kunsa, bayan da Janar Assimi Gota da mukarabansa masu kakin soja suka mari wuka da nama a cikin harkokin gudanarwa a fadar mulki ta Koulouba. Batun shirya zaben ya kunno kai domin martaba daya daga cikin alkawuran sojojin, bayan da ya haifar da kiki-kaka  da kai ruwa ranan da ya yi silar raba gari tsakanin Goita da tsohon firaminista choguel Kokala Maiga.

Karin bayani: Zargin take hakkin dan Adam a Mali

Choguel Kokalla Maïga ya raba gari da gwamnatin Mali saboda rashin shirya zabe
Choguel Kokalla Maïga ya raba gari da gwamnatin Mali saboda rashin shirya zabeHoto: Website des Premierministers Choguel Kokalla Maïga

Dama 'yan siyasa a kasar Mali musamman ma masu bibiyar gwamnatin Bamako irin su Abdrahmane Diarra na jam'iyyar URD, suka ce yanzu gari ya waye. Ya ce: " Mun san da cewa ba makawa komai daren dadewa gwamnatin rikon kwarya za ta aiwatar da wasu humminan sauye-sauyen da za su hada da shirya zabe, da mika ragamar kasar ga sabon jagora da zai mulke ta, ta hanyar zabe, saboda haka wannan shelar ma dai na nufin ne kawai Shugaba Goita na kan turba madaidaiciya. Za a zakulo hanyoyin da suka dace na shirya zaben da zai mika mulki don kawo karshen gwamnatin rikon kwarya."

Wai shin Bamako na shirin komawa turbar dimukuradiyya?

Matakin gwamnatin Mali ba ya rasa nasaba da kokarin da take yi na ganin ta kawo karshe cece-kucen da ya ki cinyewa a tsakaninta da 'yan siyasa na cikin gida, a dangane da yawaita dage ranakun zabe da ma zubar da kimarta kan alkawuran zaben a idon duniya. Oumarou Ibarhim Toure, shugaban kawancen APR ya ce idan ma akwai wannan manufar shirya zabe, amma akwai muhimman hannyoyin da ya dace a bi domin kaiwa ga gabar zaben.

Za a yi zaben gama gari bayan zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin Mali
Za a yi zaben gama gari bayan zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin MaliHoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Ya ce " Muna da sabon kundin tsarin mulki, wanda ke tattare da dokokin tsara zabe, wadannan dokokin na jibe a teburin shugaban hukumar koli ta mulki soji ba tare da kaddamar da su ba. Akwai bukatar a hanzarta amfani da wannan dokokin, a  kuma rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe da ta zo daidai da kundin tsarin mulkin shekarar 2023. A matsayina na dan siyasa, ina ganin ya dace a ce shugaban kasa ya gana da jam'iyyu don tattauna wannan batu da ma dai wasu batutuwa da dama musamman na kayyade lokutan zabe."

Karin bayani: An tattauna matsalolin Mali

Babu wata ranar da aka kayyade a hukumance don gudanar da zaben kasar ta Mali. Sai dai da dama na ganin cewar shugaban kasar na kan hanyarsa ta cika wannan alkawari ta hanyar neman mafita, inda a cikin tsarin ministoci ,Shugaba Goita ya kafa ma'aikata ta musamman kan harkokin sake fasalta tsare-tsaren siyasa da dafa wa tsare-tsaren zabe. Akwai dai alamomin da ke kara tabbatar da cewa, an kama hanyar kawo karshen gwamnatin rikon kwarya a kasar Mali.