Assad ya naɗa sabon Firayim Ministan Siriya
August 9, 2012Shugaba Bashar al-Assad na ƙasar Siriya ya naɗa sabon Wael al-Halqi a matsayin sabon Fira Ministan ƙasar, kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar ta bayyana.
Sanarwar ta ce Shugaba Assad ya saka hanu kan ayar doka mai lamba 298, da ta amince da naɗin al-Halqi kan muƙamun na Fira Minista, kuma kafin yanzu shi ne ministan kula da harƙoƙin kula da kiwon lafiya.
Tsohon Fira Ministan ƙasar ta Siriya Riad Hijab ya sauya sheƙa inda ya koma ɓangaren 'yan adawa ranar Litinin da ta gabata. Kuma yanzu haka yana ƙasar Jordan shi da iyalansa.
A wani labarin mayaƙan 'yan tawayen ƙasar ta Siriya, yau Alhamis, sun fice da cikin ɗaukacin yankin Salaheddin na arewacin birnin Aleppo, inda ake ci gaba da bata kashi tsakaninsu da dakarun gwamnati.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu