1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Assad: Za mu kwato arewacin Siriya

Ahmed Salisu
June 24, 2018

Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya ce sojin kasar za su yi amfani da karfi wajen karbe iko da arewacin kasar muddin 'yan tawaye suka ki mika wuya kana suka ki amincewa da shirin wanzar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/30B6l
Bashar al-Assad | Syrischer Präsdident
Hoto: Reuters/Sana

Shugaban ya ambata hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin din nan na NTV na kasar Rasha inda ya ke cewar gwamnati ba ta son amfani da karfi amma idan 'yan tawayen suka yi kunne kashi to sojin za su kasance ba su da wani zabi illa su murkushesu. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da dakarun gwamnati ke kokari na fatattakar 'yan tawayen daga kudancin kasar, inda a jiya aka bada labarin cewar sun karbe iko da garin nan Deraa da a baya 'yan tawayen ke rike da shi.