1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaGabas ta Tsakiya

Bikin sallar Ashura a kasashen Larabawa

Mahmud Yaya Azare SB
July 16, 2024

Lokacin da Musulmi mabiya mazhabobin Sunnah ke Azimin Ashura da sallar cika ciki, ana ci gaba da tsangwamar Musulmi mabiya mazhabar Shia da ke zaman makoki a ranar sallar ta cika ciki a wasu daga cikin kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/4iNwP
Irak | Masallacin Karbala
Masallacin KarbalaHoto: Karar Essa/AA/picture alliance

Azumin Ashura da Sallar ciki ciki na daya daga cikin lamuran ibada a musulunci da aka jima ana samun takaddama kansu tsakanin manyan bangarorin addinin musulunci biyu, wato duniyar Sunna da Shi'a.  A duniyar Sunan dai, ranar ta Ashura rana ce da Musulmi ke azumta don koyi da ma'aiki wanda ya ce yana yin haka ne, domin murna da halaka Fir'auna da aka yi, a lokacin da yake kokarin ganin bayan Annabi Musa da mabiyansa.

Karin Bayani: Arangama da 'yan Shi'a a Najeriya

Masu bikin Ashura a Bahrain
Masu bikin Ashura a BahrainHoto: Hamad I Mohammed/REUTERS

Koma dai ya ake ciki, tuni mazauna zirin Gaza na Falasdinu da ke fama da yunwa a ranar ta sallar cika ciki da ake yalwata iyali, sakamakon hana shigar musu da kayyakin agaji da Isra'ila ta yi, sukai fata kan samun sauki. Shi kuwa Hassan Nasarullah na kungiyar Hezbollah kira ya yi ga Musulmun duniya da su dauki ranar a matsayar ranar koyi da Imam Husaini wajen yin bore ga azzulumai ko'ina suke a duniya:

To sai dai a hannu guda, a kasar Oman, wasu masu matsanancin ra'ayi sun bude wuta kan wani masallacin yan shi'a da ke zaman makokin kashe jikan ma'aiki Sayyidina Husaini, a yayin da a kasar Kuwaiti aka hana tattaki da kafa tutocin ranar Karbala a kofar gidajen jama'a, kan ban da kofar masallatan yan shi'a.