1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ashton Carter ya isa Iraki don daukar matakai akan IS

Kamaluddeen SaniDecember 17, 2015

Sakataren harkokin tsaron Amirka Ashton Carter ya isa garin Arbil a yau alhamis domin gudanar da wata tattaunawa da jami'an Kurdawan Iraki a dangane da batun yakar kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/1HPCA
USA Verteidigungsminister Ashton Carter
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Wolf

Ziyarar Ashton Carter a Arbil babban birnin yankin Kurdawa dake a Iraki na zuwa ne bayan ziyarar daya kai a Baghdad, a inda ya gana da Firiministan Irakin Haider al-Abadi kan yadda zasu kara yaukaka danganta a tsakanin su ta fuskar samarwa dakarun horaswa da makamai.

Jiragen yakin Amirka dai na kai hare-hare ta jirage akan mayakan IS da mafiya yawansu suke a Syriya da Iraki tare da cigaba da ja musu kunne kan danke shugabani su don kawar da kungiyar kwata kwata daga doran kasa.