Asarar rayuka a Somaliya
April 7, 2017Talla
Harin na rokoki cikin gundumar Wadajir da ke Mogadishu babban birnin kasar ta Somaliya, a cewar jami'an 'yan sanda mata uku ne a gida daya suka mutu yayin da wasu mutanen biyar kuwa suka jikkata.
Harin wanda ya shafi yankin da ke kusa da filin tashi da saukar jirage na birnin, na zuwa ne kwana guda da sauya jagabannin tsaro da gwamnatin kasar ta yi.
A jiya Alhamis ne Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohammed ya sauya manyan hafsoshin tsaro, ya kuma yi kiran mayakan Al Shabab da su yi saranda cikin kwanaki 60. Tuni ma jami'an 'yan sandan Somaliya suka dora alhakin harin kan mayakan Al Shabab.
Sai dai ba a sami martanin Al Shabab din da ake zargi ba, amma a baya ta sha daukar alhakin irin wadannan hare hare a kasar.