1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun yi artabu da masu bore a Girka

Abdoulaye Mamane Amadou
March 5, 2023

Kwanaki bayan mummunan hadarin jirgin kasa da ya halaka mutane 57 dubun-dubatar masu bore sun yi artabu da 'yan sandan kwantar da tarzoma a Girka.

https://p.dw.com/p/4OH0w
Griechenland Proteste
Hoto: Eurokinissi/ZUMA Wire/IMAGO

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi artabu da dubban masu zanga-zanga da suka yi dandazo a harabar majalisar dokoki ta birnin Athenses a wannan Lahadi, kwanaki bayan mummunan hadarin jirgin kasa da ya halaka mutane 57.

Masu boren sun yi ta kone-konen kwandunan shara da jefa wa 'yan sanda wasu abubuwan fashewa, a yayin da su kuwa jami'an tsaron, suka yi ta harba gurnetin hayaki mai sa kwalla don tarwatsa zanga-zangar.

Wannan lamarin na zuwa ne duk da binicken da hukumomin kasar suka fara kan hadarin na wannan makon, inda yanzu hakan wani alkali a birnin Larissa ya bukaci a gurfanar da shugaban babbar tashar jiragen kasa na kasar bisa tuhumarsa da yin sakacin da ya kai ga  mutuwar al'umma.

Bayan jagoran akwai yiwuwar a gurfanar da shugabannin kafanin sufurin jiragen kasar ta Girka na "Hellenic Train" a cewar wasu majiyoyin shari'ar kasar.