Amirka ta bude ofishin jakadancinta a Birnin Kudus
May 14, 2018A daidai lokacin da Amirka ta gudanar da shagulgulan bude ofishin jakadancinta na kasar Isra'ila a Birnin Kudus, dakarun sojin Isra'ila sun bindige gwamman Falalsdinawa a yankin Gaza, a yayin da suka yi kokarin kutsawa yankunansu da Isra'ila ta mamayae tun shekaru 70 din da suka gabata.
Motocin agaji sun yi ta kwashe gwamman gawawwaki da daruruwan masu raunukan da dakarun sojin Isra'ila suka dinga yin harbin kan mai uwa da wabi kan dandazonsu.
Kakin sojin Isra'ila ya ce sun dauki wannan matakin ne don kare kai.
"Mun ji kiraye-kiraye karara daga kungiyar Hamas da sauran 'yan ta'adda kan za su mamaye Isra'ila su sharemu daga doran kasa, don haka ne sojojinmu suka mai da martini. Har yanzu a shirye muke mu dauki tsauraran matakai fiye da wanda muka dauka don kare kanmu."
Shugaban kungiyar Hamas Ibrahim Haniyya, wanda ya siffanta wadanda suka kwanta daman da gwarazan shahidai da suka yi shahada a yayin kokarin 'yanta yankunansu da aka kori kakaninsu daga cikinsu tun shekaru 70 din da suka gabata, ya ce ta'addancin Isra'ila da wuce gona da irinta, ba zai sanya su dangana su saryantar da hakkokinsu ba.
"Al'ummar a yau ta fito ke nan ba komawa, ko dai dukkaninmu mu yi shahada, ko kuma mu ga bayan mugun tanadin Trump na mamaye Birnin Kudus, sai kuma munga al'ummar Falasdinawa ta koma yankunansu da aka kwace musu."
Wannan tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka ke shagulgulan bude ofishin jakadancin a Birnin na Kudus, bikin da kimanin mutane 800 suka halarta, cikinsu har da Ivanka Trump, diyar Shugaban Amirka Donald Trump da mijinta Kushner, a yayin da Trump ya yi jawabin taya murna ga Isra'ilan ta kafar bidiyo, inda ya jaddada al'amarin a matsayin cika alkawarin da ya yi a watan Disamba na 2017.
Shugaban Falalsdinawa Mahmud Abbas, wanda yake fuskantar matsin lamba daga 'yan uwansa larabawa kan ya mika wuya bori ya hau, ya amince da Birnin Abu Nees a matsayin Fadar mulkin Falasdinawa, ya siffanta ranar ta yau da ranar Nakbah ta biyu, wato ranar saukar bala'i na biyu ga al'ummar Falalsdinu.
Tun daga shekarar 1967 ne Isra'ila ta mamaye gabashin Birnin Kudus lokacin da aka yi yaki a Gabas ta Tsakiya. Sai dai ba bu wata kasa da ta amince da haka sai lokacin da shugaban Amirka Trump ya ayyana aniyyar kasarsa a watan Disambar shekarar 2017, ta komawa birnin, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da shi.