1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Argentina ta lashe gasar kwallon kafa ta duniya

December 18, 2022

Kasar Argentina ta yi nasarar lashe gasar kwallon kafa ta duniya da aka kammala a wannan Lahadi a kasar Katar. Ta yi nasara ne a kan kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/4L8Ul
Hoto: Julian Finney/Getty Images

Argentina ta ci abokiyar karawarta Faransa ne da ci 4:2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan tashi wasan mintuna 120 da suka yi da 3:3.

Da farko dai Argentina ce ta ci Faransa biyu da nema kafin tafiya hutun rabin lokaci, sannan Faransar ta farke bayan komawa fili.

Keftin din kasar Argentina Lionel Messi, ya cika burinsa na daga kofin duniya a karshen wasansa a wannan mataki da ya hada kasashen duniya.

Tauraron dan wasan Faransa Kylian Mbappe, ya ci kwallaye uku rigis a ragar Argentina, biyu daga cikin kwallayen kuma ya same su ne ta hanyar fenariti.

Karo na uku ke nan da Argentina ke daukar kofin duniya, kasancewar ta dauka a shekarar 1978 sannan ta maimaita a 1986, sai ga shi kuma ta samu a wannan lokaci.