1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bukatar sakin Bazoum da iyalansa

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna damuwa matuka, kan rahotannin halin tasku da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da ilyalansa ke ciki.

https://p.dw.com/p/4V0Vr
Majalisar Dinkin Duniya | Sakatare Janar | Antonio Guterres | Nijar | Juyin Mulki
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: Ed Jones/AFP

Cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar, ya nunar da cewa sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya damu matuka kan yanayin lafiya da ma tsaron shugaban  Jamhuriyar Nijar din da iyalansa. Ya kuma yi kira ga sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata, kan su gaggauta sakin sa shi da iyalan nasa ba tare da wani sharadi ba su kuma mayar da shi kan kujerarsa.