1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antonio Guterres na ziyara a kasar Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
March 8, 2023

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi daga kasar Ukraine na da matukar muhimmanci.

https://p.dw.com/p/4OPtg
USA New York | UN-Vollversammlung | Antonio Guterres
Hoto: Eduardo Munoz/REUTERS

Guterres wanda ke ziyarar aiki a birnin Kyiv na kasar Ukraine ya ce akwai bukatar ci gaba da yarjejeniar da aka cimma a baya da kasashen Rasha da Ukraine, ta fidda hatsi ta tekun Baharul Aswad.

Shi ma a nasa bangaren Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine din, ya ce sabunta wannan shiri na da matukar muhimmanci ga duniya baki daya.

Tun bayan cimma matsaya a kan fitar da hatsin da ke jibge a tashoshin ruwan Ukraine, yanzu haka an sami damar fidda sama da tan miliyan 23 ya zuwa kasashen duniya.

karkashin wannan yarjejeniyar da aka cimma a shekarar da ta gabata , Rasha na iya fitar da takin zamani duk da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba mata, sai dai Rasha na kukan cewa ba duka yarjejeniyar aka mutunta ba, matakin da ake ganin ka iya kawo cikas ga dorewar wannna shiri da aka samar da tallafin kasar Turkiyya da MDD.