SiyasaAfirka
Annobar corona ta dauki hankalin taron G7
May 5, 2021Talla
A yayin da ake shirin kamalla taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki wato G7, batun kamanta daidaito a yakar annobar coronavirus zai kasance batun da mahalarta taron za su fi mayar da hankali a wannan Laraba. An dade ana zargin rashin yin adalci a kasafta rigakafin allurar inda kasashe marasa karfi suka sami kaso kalilan na rigakafin.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ma, ta yi wannan kira, a daidai lokacin da kasashe matalauta ke fama a yakin da suke da annobar, ta ce ya zama wajibi a rage wannan wagegen gibin da aka samu, don sai da haka, za a iya guduwa tare, don a tsira tare. Corona ta kama sama da mutum miliyan talatin a fadin duniya tun bayan bullarta a Disambar 2019.