1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya zargi Siriya da rashin aiwatar shirin Sulhu

April 12, 2012

Shugabannin Duniya na ci gaba da kira ga Siriya da ta mutunta wa shirin tsagaita wuta tare da aiwatar dashi bisa ga yarjejejiya

https://p.dw.com/p/14dCo
Kufi Annan Bildbeschreibung: Der UN Sonderbeauftragte spricht in Theran mit iranische Regierung über Syrien Stichwörter: Iran, Land und Leute, KW15 /12, Politik, Annan, Salehi, Syrien Quelle: FARS Lizenz: Frei
Hoto: Fars

Shugaba Barack Obama na Amurka da takwaransa Nicolas Sarkozy na Faransa, sun yi kira ga Siriya da ta mutunta wa shirin Majalisar Ɗunkin Duniya na kawo ƙarshen asarar rayuka da ƙasar ke fuskanta, kokuma a ɗauki tsauraran matakai na kawo karshen rikicin. A wata sanarwar da suka gabatar bayan ganawa, shugabannin biyu kazalika sun yi kira ga Iran data ɗauki matakan shawarwari, ayayin taron manyan kasashe masu fada aji a birnin Istambul ranar juma'a. A wannan alhamis din ne dai jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya da ƙasashen larabawa, Kofi Annan ya shaida wa Komitin sulhu cewar, Siriya bata aiwatar cikakken shirin warware rikicin kamar yadda aka tanadar ba, akan haka ne yayi kira ga komitin mai wakilai 15, daya bukaci janyewar dukkan sojojin Siriya da makamasu daga biranen kasar.

Daura da taron ministocin harkokin waje na kasashen G8 a washington, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bukaci da a bawa shirin warware rikicin Siriyar dama. A gobe Juma'a ne dai manyan kasashen Duniya masu fada aji, zasu gudanar da ganawarsu ta farko da Iran sama da shekara guda, tare da fatan cewar Tehran zata bada isassun bayanai dangane da shrin nukiliyarta, wanda hakan ne zai kawar da barazanar yaki a yankin gabas ta tsakiya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal