1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya yi nasara ciwo kan Sudan ta amince da Dakarun MDD a yankin Darfur.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bubf

Sakatare jannar nan Majalisar Ɗinkin Dunia Kofi Annan, ya cimma burin sa na shawo kann hukumomin Sudan, su amince da karɓar dakarun kwantar da tarzoma na Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfour.

Annan ya cimma wannan buri, bayan doguwar tantanawar da yayi jiya, tare da wakilin gwamnatin Sudan , da na ƙungiyar tarayya Afrika,a birnin Adis Ababa na ƙasar Ethiopia.

Bayan adawar da ta nuna, a halin yanzu, Sudan ta bada kai bori ya hau, ta hayar amincewa MDD, ta aika dakarun ta, domin su ƙara ƙarfin gwiwa, ga na ƙungiyar taraya Afrika a yankin Darfur.

Saidai tantanawar, ba ta haƙiƙance yawan dakarun MDD ba, da kuma lokacin da su zuwa yankin na Darfour.

Wannan yarjejniya, na ɗaya daga mahimman nasarorin da Koffi Annan ya cimma, a yayin da ya rage masa, wata ɗaya kaccal, ya sauka daga muƙamin sa, na Sakatare jannar.