1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta yaba ziyararta a Ƙasar Sin

February 4, 2012

Ƙasashen Jamus da Sin sun jaddada ƙudirin haɓaka dangantakar kasuwanci da na diplomasiyya da ke tsakaninsu

https://p.dw.com/p/13x8z
German Chancellor Angela Merkel (L) shakes hands with Chinese Premier Wen Jiabao at the end of a news conference at the Great Hall of the People in Beijing February 2, 2012. Merkel on Thursday urged China to use its influence to persuade Iran to give up its nuclear programme, at the start of a three-day visit when she will also seek China's support for the ailing euro. REUTERS/Adrian Bradshaw/Pool (CHINA - Tags: POLITICS)// eingestellt von se
Angela Merkel da Hu JintaoHoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana ziyarar rangadi ta kwanaki uku da ta kai ƙasar Sin da cewa ta yi aramashi matuƙa. Sai dai kuma ta baiyana damuwa akan matsayin haƙƙin bil Adama a ƙasar. Bayan ganawa da manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da Firimiya Wen Jiabao da kuma shugaban ƙasa Hu Jintao, Angela Merkel ta kuma tattauna da shugaban gundumar Guangdong. Ta baiyana farin ciki da ziyarar tana mai cewa " Ta ce sabon al'amari shine cewa China a shirye take ta yi aiki da tarayyar Turai da kuma taimakawa ta fannoni da dama. Za mu ƙara tattauna cikakkun bayanai akan wannan a nan gaba".

A nasa ɓangaren shugaban China Hu JIntao yace ƙasashen biyu na fatan ƙarfafa dangantaka da fahimtar juna a tsakaninsu. Shima Firimiyan ƙasar ta Sin Wen Jiabao ya tabbatarwa da shugabar gwamnatin ta Jamus amannar Beijin akan takardun kuɗin bai ɗaya na euro. Yana mai baiyana ƙudirin China na taimakawa wajen shawo kan matsalar bashi da ta dabaibaye ƙasashe masu amfani da kuɗin na euro.

A waje guda kuma 'yan sanda sun hana wani fitaccen lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil Adama halartar liyafar da aka shirya a ofishin jakadancin Jamus dake Beijin. An dai gaiyaci Mo Shaoping ya halarci liyafar wadda shugabar gwamnati Angela Merkel ta kasance babbar baƙuwa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi