1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta yi sakon taya murna ga 'yan kasar

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
December 31, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi jawabin sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ga Jamusawa inda ta bukace su da su kasance masu kyakkyawan fata da sauyi ga dabi'unsu.

https://p.dw.com/p/3VWhz
Angela Merkel Neujahrsansprache SPERRFRIST
Hoto: Reuters/M. Tantussi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga 'yan kasar Jamus da su kasance masu kyakkyawan fata kana kuma ta bukace su da su kawo sauyi ga wasu daga dabi'unsu na yau da kullum.

A yayin wani jawabinta da ke matsayin sakon taya murnar shiga sabuwar shekara wanda a ciki ta tabo batutuwa da dama, Merkel ta bayyana cewa mukan iya aiwatar da muhimman sauye-sauye idan har muka dauki kudurin samar da sababbin abubuwa masu tasiri ta fannoni da dama.

Merkel ta yi kiran 'yan kasar da su kara himma wajen yakar sauyin yanayi inda ta ce dumamar yanayi abu ne da ke a zahiri.