1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anan da Obasanjo da Biya sun gana game da yankin Bakassi

May 11, 2005

fafutikar mallakar yankin Bakassi mai albarkacin man fetur a tsakanin Nigeria da Kamaru

https://p.dw.com/p/BwUd
Hoto: AP

Shugabannin kasashen Nigeria wato Olesegun Obasanjo dana Kamaru Paul biya sun amince da daukar matakan gaggawa na kawo karshen saka sato katsin dake tsakanin su akan yankin Bakassi mai arzikin man fetur.

Wannan kalamin kuwa ya fito ne daga bakin babban sakataren mdd Kofi anan jim kadan bayan wata ganawa da yayi da shugabannin kasashen biyu a Birnin Geneva a yau laraba.

A cewar babban sakataren a yanzu haka shugabannin biyu zasu mayar da hankalin su wajen warware tsaiko da ake fuskanta na janyewar sojojin Nigeria daga yankin a hannu daya kuma da batun shata jadawalin iyaka a tsakanin kasashen biyu.

Anan ya kara da cewa shida kansa zai kasance mai sa ido game da ganin an aiwatar da wan nan yarjejeniya da aka cimma a tsakanin shugabannin kasashen biyu,da zarar mdd da shugaba Obasanjo da kuma Paul Biya sun fitar da jadawalin yadda za a aiwatar da aikin a aikace.

A dai tsari na can baya tarayyar Nigeria an shirya cewa zata janye dakarun sojin ta daga yankin na Bakassi a watan satumba na shekarar data gabata amma kuma hakan bai samu ba.

A dai watan daya gabata kasashen biyu sun cimma matsaya guda game da warware wan nan rikici daya ki ci yaki cinyewa a tsawon lokaci.

Duk dai da wannan rikici da kasashen biyu suke fuskanta,Kofi Anan ya yabawa shugabannin kasashen biyu bisa irin namijjin kokarin da suke wajen ganin an warware wan nan takaddama data dade tana ciwa kasashen biyu tuwo a kwarya.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan rikici na yankin na Bakassi mai albarkacin man fetur ya samo asali ne daga yadda kasashe yan mulkin mallaka suka shata iyakokin kasashen biyu tun daga wancan lokaci.

Bisda irin danbarwar kuwa data wanzu a tsakanin juna, ya haifar mahukuntan kasar Kamaru gurfanar da kasar ta Nigeria a gaban kuliya a kotun kasa da kasa dake birnin Hugue a watan oktobar shekara ta 2002.

Bayan wani dogon lokaci da aka dauka ana muhawara game da wan nan kara, kotun ta yanke hukuncin mika wan nan yanki na Bakassi izuwa hannun mahukuntan kasar Kamaru.

A lokacin da kotun ta yanke wan nan hukunci Nigeria tayi alkawarin yin biyya ga wan nan hukunci,to amma duk da haka sai ya kasance kasar na yin wasa da hankalin hukuncin ta hanyar kin janye sojojin ta daga yankin kamar yadda kotun ta bukaci tayi.

Rahotanni dai a yanzu haka na nuni da cewa dubbannin mutane yan Nigeria da sukayi kaura daga yankin izuwa cikin kasar kamaru a shekara ta 2001 bayan da rikicin yankin yayi tsamari a yanzu haka sun fara dawowa izuwa gida.

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta Nigeria a yanzu haka ana sa ran dawowar tawagar mutanen ta karshe izuwa gida da yawan su ya tasamma a kalla dubu goma daga cikin mutane dubu talatin da biyar da aka kiyasta sun bar yankin a lokacin da wan nan rikici ke kann ganiyar sa.