1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana zargin sace abinci a yankin Tigray

Binta Aliyu Zurmi
June 18, 2023

Rahoton binciken a kan sace kayan abinci a yankin Tigray na Habasha ya nuna cewar akwai hannun wasu jami'an gwamnatin yanki da na tarayya da ma wasu sojojin Eritrea.

https://p.dw.com/p/4Sjga
Hukumar abinci ta MDD ta saba raba kayan masarufi a yankin TigrayHoto: Ashraf Shazly/AFP

An fara binciken bayan da manyan kungiyoyin agaji na USAID da kuma hukuumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya  suka dakatar da kai dauki bayan da aka gano abincin da suka samar a kasuwannin kasar ana sayar da su. Binciken ya gano cewar an sace sama da tan dubu 7 na alkama da kuma litar mai sama da duubu dari biyu.

Sama da mutum miliyan biyu ne suka dogara da wannan dauki a kasar da ke zama ta biyu a yawan al'umma a nahiyar Afirka.