Ana zaman jiran baiyana sakamakon zaɓe a Masar
June 21, 2012Talla
Masu aiko da rahotannin sun, ce za a sami jinkiri ne aboda ƙorafe ƙorafen da yan takarar guda biyu Mohammed Morsi da kuma Ahmed Chafik suka shigar a kan sakamakon zaɓen zagaye na biyu a mazaɓu da dama.
Yanzu haka dai dubun dubatar jama'a na ci gaba da jan daga a dandali tahrir a daidai lokacin da rashin tabas kan lafiyar tsohon shugaban ƙasar wato Hosni Mubarak ke ƙaruwa.Wani wanda ke a dandalin tahrir ɗin ya shaida cewar Morsi muke so ya ce idan Allah ya yi ba zamu tashi daga nan ba sai an bayana shi a matsayin shugaban ƙasa,ya ce ba za mu yarda ba ,da murɗi na sojoji.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh