Guinea-Bissau za ta samu sabbin 'yan majalisa
June 4, 2023Talla
Masu zabe kimanin 900,000 na can na zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Guinea-Bissau. Fafatawar ta fi zafi a tsakanin jam'iyyar PAIGC da ta yi kokarin wajen samun 'yan cin kan kasar da kuma Madem-G15. Masu sanya ido daga ciki da wajen kasar sama da 200 ne ke duba yadda zaben ke gudana. Ana sa ran rufe rumfunan zaben da mislain karfe biyar na yamma agogon kasar.
Rikicin da yanzu haka ya fi daukar hankalin 'yan kasar shi ne takaddmar da ta barke kan bukatar da Shugaba Embalo ya mika wa majalisar da aka rushe bara ta gyaran kudin tsarin mulki.