1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun karin mace-mace a Siriya

February 6, 2012

Burtaniya ta kira jakadanta dake Siriya gida, domin ganawa da shi, a wani mataki na nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na murkushe masu zanga-zanga, inda akalla mutane 46 suka hallaka

https://p.dw.com/p/13yD8
Demonstrators protest against Syria's President Bashar al-Assad in the town of Hula near the city of Homs February 3, 2012. Picture taken February 3, 2012 REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS) THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS
Masu zanga-zanga a birnin Homs na kassar SiriyaHoto: Reuters

Dakarun Siriya sun yi ruwan rokoki kan wuraren da masu zanga-zanga suke taruwa, abun da ya yi sanadiyyar akalla rayuka 46 bisa rahotannin masu rajin kare hakkin bil adama. Majalisar wucin gadin 'yan adawar Siriyar ta ce dakarun gwamnatin sun yi wa garin Homs Kawanya da tankokin yaki suna dammarar yi mata kutse kuma sun yi gargadin aukuwar kisar kiyashi a babban birnin kasar.

Burtaniya ta kira jakadanta dake Siriya gida, domin ganawa da shi, a yayin da gwamnatin kasar ke cigaba da murkushe masu zanga-zanga. A wata sanarwar da ya gabatarwa Majalisar dokokin kasar bayan da kasashen Rasha da China suka dare kujerar naki wajen amincewa da kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen Burtaniyan William Hague, ya ce sun kira jakadan ne domin su nuna rashin goyon bayansu ga abun da ke faruwa a Siriya.

Haka nan kuma kungiyar Tarayar Turai ita ma tana shirya sabbin takunkumin da zata kakabawa Siriyar kasancewar shirin aiwatar da kudurin kwamitin sulhun ya ci tura. Kasashen suna tattauna wadannan matakan ne gabanin taron ministocin wajen turan wanda za'a gudanar ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu.

Kasashen Faransa da Burtanniya kuma sun riga sun bayyana aniyarsu na matsawa EU lamba domin ta dada taurara matakai dan nuna adawa da gwamnatin Bashar al-Assad.

Dama dai kungiyar ta riga ta sanya shugaba Bashar al-Assad da wasu na hannun damansa a cikin jerin sunayen wadanda aka haramta masu takardun tafiya, wato visa sun kuma dora hannu kan kaddarorinsu sa'an nan sun kuma sanya mata dokar haramci kan cinikin man fetur da makamai.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Ahmad Tijani Lawal