1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana hawan Arfa a cikin yanayin covid-19

Mouhamadou Awal Balarabe
July 30, 2020

Musulmi da ke sauke farali a kasar Saudiyya na gudanar da hawan Arfa a wani mataki na mutunta daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji, a daidai lokacin da kasa mai tsarki ke yaki da nnobar corona.

https://p.dw.com/p/3gAz8
Saudi-Arabien Hadsch-Wallfahrt in Mekka
Hoto: picture-alliance/dpa/CIC

 An kafa shingayen tsaro a kewayen dutsen Arfr domin hana yaduwar cutar corona tsakanin maniyatan da ke hawan arfa. Gidan talabijin na kasar Saudiyya ya ruwaito cewa an yi ta jigilar mahajjatan da bos daga Minna bayan da suka sanya kyallen rufe baki da hanci.

Hukumomin Saudiyya sun kayyade mazauna kasar dubu 10,000 kacal, a matsayin mutanen da za su yi ibadar ta bana, amma ba tare da amincewa da kowa daga ketare ba sakamakon bullar annobar covid-19. A kasa mai tsarki dai mutane akalla dubu 272,590 ne suka  kamu da covid-19, ciki har da mutum 2,816 da cutar ta yi sanadiyyar mutuwarsu.

Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci da ake so kowanne Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwarsa idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya. Daga cikin irin ayyuka da Musulmi ke gudanar a wannan jajiberen sallar layya har da yin azumi, ga wadanda ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba.