1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Ana gudanar da zabe a kasar Pakistan

Suleiman Babayo MAB
February 8, 2024

Milyoyin mutane suna kada kuri'u a zaben kasar Pakistan yayin da hukumomi suka katse layukan wayoyin hannu a Pakistan yayin da ake zaben kasa baki daya.

https://p.dw.com/p/4c9cJ
Masu zabe na Pakistan
Masu zabe na Pakistan Hoto: BANARAS KHAN/AFP

Milyoyin mutane suna kada kuri'u a zaben kasar Pakistan na kasa baki daya da ke gudana a wannan Alhamis. An dai samu tashe-tahsen hankula na hare-hare gabanin zaben da ake gudanarwa. Hukumomin kasar suka katse sadarwar wayoyin hannu a fadin kasar domin dakile duk wani yunkurin kawo cikas ga zaben da ake yi.

Akwai masu zabe kimanin milyan 128 a kasar da ke da jama'a kimanin milyan 240. Masu sharhi kan kasar ta Pakistan suna ganin akwai yuwuwar tsohon Firaminista Nawaz Sharif ya sake dawowa kan madafun iko saboda goyon bayan da yake samu daga sojoji wadanda suke da tasiri a harkokin siyasar kasar. Haka na zuwa lokacin da shi kuma tsohon Firaminista Imran Khan yake garkame a gidan fursuna sakamakon wasu tuhume-tuhume da ake gani suna da dangantaka da siyasa. Kana a takarar neman mukamun na firaminista akwai Bilawal Bhutto Zardari wanda mahaifiyarsa Marigayiya Benazir Bhutto ta kasance tsohuwar firaminista.

Gaba daya majalisar dokokin kasar ta Pakistan tana da kujeru 266 da ke takara kuma duk jam'iyyar da ta samu galibin kujerun za ta kafa gwamnati da kawance.