Ana gudanar da bincike a Siriya
July 15, 2012Talla
A cikin wata sanarwa da ya baiyana wani mai magana da yawun tawagar ya ce sun ga gidaje da makarantu da aka ƙone ƙurmus, sannan kuma jini na zube barjat koi'na a cikin gidajen.'Yan adawar na Siriya sun ce mutane sama da ɗari biyu suka rasa rayukansu a cikin farmakin, to amma tawagar ba ta tabbatar da addadin ba. Sai dai ta ce sojojin gwamnatin sun yi amfanin da muggan makamai.
Ƙasashen Jamus da Ingila da Amirka da Faransa da Portugal sun gabatar da wani ƙudirin doka ga MDD, wanda ke bai wa shugaba Assad wa'adin ƙwanaki goma na ya dakatar da yin amfani da manyan makama, wajan kai hare hare akan al' ummarsa, ko kuma ya fuskanci ƙarin takunkumi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas