1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da atisayen sojin NATO

October 31, 2018

Kasar Jamus za ta aika da wakilci lokacin wani atisayen sojin kungiyar tsaro ta NATO da za a yi a kasar Norway.

https://p.dw.com/p/37RKU
Nato-Großübung "Trident Juncture" in Norwegen
Hoto: picture-alliance/dpa/Digital/Nato/sgt M. A. gaudreault

Ministar harkokin tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen, za ta kai ziyara kasar ta Norway, inda ake wani gagarumin atisayen soji na kungiyar tsaro ta NATO da ba ga irinsa ba tun bayan yakin cacar baka.

Atisayen mai dakaru dubu 50, da dubban motoci gami da jiragen yaki, aiki ne da aka fara shi tun cikin makon jiya.

Lamarin ya kuma shafi inganta dabarun yaki da suka hada da na mayakan kasa da na sama da na ruwa da ma na wasu hanyoyin sadarwa na zamani.

Ministar ta tsaron Jamus, za kuma ta ziyarci sansanin sojojin Jamus wanda ke kusa da filin jirgi na birnin Oslo.

Akalla dakarun Jamus dubu takwas na daga cikin wadanda ke halartar wannan atisayen.