1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farautar mutumin da ya daba wa Jamusawa wuka Solingen

Binta Aliyu Zurmi ZUD
August 24, 2024

Jami'an tsaro sun ce daga cikin wadanda harin ya jikkata mutane biyar na a cikin mawuyacin hali bayan faruwar lamarin a birnin Solingen.

https://p.dw.com/p/4jsuM
Hoto: Federico Gambarini/dpa/picture alliance

Jami'an tsaro a Jamus na ci gaba da neman wani mutum ruwa a jallo bisa zargin sa da jaka wa mutanewuka a wani mummunan farmaki da ya hallaka mutane uku ya kuma jikkatawasu takwas a garin Solingen da ke jihar North Rhine Westafalia a yammacin kasar.

Tun wayewar garin Asabar aka baza 'yan sanda har da masu farin kaya gami da jirage masu saukar ungulu domin gano mabuyar maharin.

An bukacin al'umma da su kasance a cikin gida sabodahadarin da ke tattare da mutumin da 'yan sanda suka ce ba su san musabbabin kai harinba.