1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisar dokokin Isra'ila

Abdourahamane Hassane
September 17, 2019

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kara mamaye wasu yankunan da ke yamma da gabar kogin Jodan. Firaministan ya bayyana haka lokacin yakin neman zabe na 'yan majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/3PjGn
Israel Wahlkampf in Bnei Brak
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Balilty

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya kara azama kan neman ganin ya lashe zaben. Shin kalaman da ya bayyana farfaganda ne domin samun goyon bayan al'umma daf da lokacin da ake ganin zaben zai kasance kankankan tsakanin Benjamen Netanyahu da kuma abokin takararsa tsohon babban hafsan hafsoshin soja Benny Gantz.

Kafin zaben dai an gudanar da yakin neman zaben cikin wani yanayi wanda kowane daga cikin 'yan takara ke fafutukar samun amincewar jama'a, musammun ma game da yadda Firaminista Benjamen Netanyahu ke kara ba da kai bori ya hau a kan bukatun Yahudawa.

Parlamentssitzung Knesset Israel Verschiebung Wahlen
Hoto: AFP/Getty Images/M. Kahana

Kididiga dai ta nuna cewar firaminista Benjamen Netanyahu na jam'iyyar Likud da shi da Beny Gantz tsohon hafsan hasoshin sojin kasar kowane daga cikinsu ba ya da tabbas na samun rinjaye a majalisar, dole sai sun nemi yin kawance,Kuma Avigdor Liberman wanda shi ne ake ganin a matsayi na uku shi zai kasance wanda zai raba gardama ga duk wanda ya mara wa baya.

Firaministan Israila Benjamen Netanyahu ya bayyana sanarwa da yake ganin inda ya yi hakan zai ci zaben yan majalisun dokokin na kara mamaye wasu yankunan gabar yamma da kogin Jodan wanda yahudawan da dama ke a wannan ra'ayi

Israel Wahlkampf 2019 | Benny Gantz, Blue and White Party
Hoto: Reuters/A. Awad

Beny Gantz dan jamiyyar masu matsagaicin raayi wanda ba shi da wasu manoufi na takamaimai a kan shaanin tsaro, na sa ran yin kawance idan har ta kama da jamiyyun siyasa wadanda ba su da nasaba da addini da na jamiyyun siyasa larabawa domin fuskantar gungun jamyyun siyasa masu rayin yan mazan jiya da na yahudawa da kuma jamiyyu maabiya addini na orthodoxe a karkashin jagorancin jamiyyar yan mazan jiya ta firaminista Benjamen Netanyahu

A cikin watan afrilun da ya gabata dai jamiyyar Likud ta Firaminista Benjamen Netanyahu da kuma jam'iyyar masu matsagaicin ra'ayi ta Kahol Lavab na jam'iyyar mai launin shudi da fari ta Beny Ganzt sun yi kunnen doki a zaben kowane na da kujeru 35. A kan haka shugaban Israila Reuven Rivilin ya bukaci firaministan da ya kafa gwamnatin kawance ta hadin kan kasa. Amma Benjamen Netanyhu ya ki haka ya rusa majalisar ya kuma kira sabon zabe bayan watanni shida.

Sai dai  idan har ya sha to kam ya tsira idan ko ya fadi babu shakka akwai tarin zarge-zarge da ake yi masa na cin hanci da rashawa wanda hakan ya kan iya sa ya fada hannun kotu.