1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka mai zanga-zanga a Sudan

Abdul-raheem Hassan SB
January 30, 2022

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Sudan sun tabbatar da cewa mutum daya ya rasa ransa cikin masu zanga-zangar adawa da mulkin sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/46HyC
Sudan | Pro-Demokratie-Demonstranten trotzen dem harten Vorgehen nach dem Putsch
Hoto: DW

Jami'an kiwon lafiya a Khartoum babban birnin kasar Sudan, sun tabbatar da mutuwar mutum daya cikin masu zanga-zanga da suka fito kan titunan kasar a wannan Lahadi saboda nuna adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi tare da neman hukunta wadanda suka kashe fararen hula a baya.

Marigayi Mohamed Yousef Ismail mai shekaru 27 a duniya, ya gamu da ajalinsa sakamakon arangama da harsashin jami'an tsaro da ke kokarin tarwatsa dandazon masu boren da ke kokarin cimma fadar shugaban kasar.

Yanzu haka dai kimanin mutane 79 suka mutu, sama da mutane 2,000 sun jikkata wasu na tsare a hannun 'yan sanda tun bayan fara zanga-zangar neman mayar da mulki ga gwamnatin farar hula a watan Oktoba.