Ana ci-gaba da zakulo mutane bayan girgizar kasa a China
September 8, 2012Rahotannin baya bayan nan sun tabbatar da mutuwar a kalla mutane 80 sakamakona wata gigizar kasar da ta faru a kasar Sin ko kuma China a karshen makon nan. Wata girgizar kasa mai karfin marki 7 da digo 6 ta kacancana wasu yankunan kudanci da yammacin kasar inda yanzu haka masu ayyukan ceto ke ci-gaba da binciken tsammanin warabbuka domin zakulo wasu mutanen da a ke saran sun bata. Yankunan kasar ta Sin ko kuma China na fuskantar yawan girgizar kasa inda ko a shekarar da ta gabata sama da mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu a makamantan wadannan haduran. Wannan al'amarin ya zo ne bayan rugujewar wata mahakar ma'adanai a arewacin kasar inda a kalla mutane 107 ne suka rasa rayukansu.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh