Ana ci gaba da yin luguden wuta a Siriya
July 30, 2012Tun da farko dai dakarun gwamnatin sun sanar sun karpe iko da wani ɓangare na unguwar Salahedine amma kuma daga bisanni yan tawayen suka musunta ikirarin.
sannan kuma yan tawyen sun ce su ƙwace garin Denadem da ke kan iyaka da Turkiya abinda zai ba su damar shigo da makamai;ministan harkokin waje na faransa ya ce ƙasarsa za ta kira wani taro na musammun.''ya ce tun da Faransa zata karɓi ragamar kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a cikin watan Augusta mai shirin kamawa;ya ce zamu kira wani taron gaggawa na ministocin harkokin waje kafin ƙarshen wannan mako.
Rahotannin da ke zuwa mana y kuma ,na cewar babban sakataran MDD Ban Ki Moon ya sanar da cewar dakarun gwamnati na Siriya sun kai farmaki ga tawagar Majalisar mai saka ido a ciki hada shugaba tawagar sai dai sanarwa ta ce babu wanda ya samu rauni a cikin su.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Auwal