1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da tarzuma a Siriya

August 31, 2011

Kawo yanzu ana ci gaba da samun asaran rayuka a Siriya inda jami'an tsaro ke karawa da masu adawa da gwamnati, abinda kuma ke ƙara jawo asaran rayuka

https://p.dw.com/p/12RFC
Jami'an sojin Siriya ke sintiri a ƙasarHoto: AP

ƙungiyoyin kare haƙin bil-Adama a ƙasar Siriya sun ce mutane 473 suka rasa rayukansu a bukukuwan sallah ƙarshen watan ramadan da aka gudanar ran litini a ƙasar. Wannan sanarwa dai ta zo ne a daidai lokacin da jami'an tsaro ke ci gaba da fatattakar jama'a a garin Homs. Sanarwa wacce wata ƙungiyar da ake kira da sunan OSDH wadda take da cibiya a Birtaniya ta baiyana, ta ce mutane 360 daga cikin addadin waɗanda suka mutun farar fula ne yayin da ake da jami'an tsaro 113 cikin wadanda suka mutun. Kana kuma ƙungiyar ta ce wasu samari da dama 'yan ƙasa da shekaru 18 sun mutu sakamakon huƙubar da aka riƙa gana masu a cikin gidajen yari. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da cewa mutane dubu biyu da ɗari biyu ne suka mutu a ƙasar ta Siriya tun lokacin da rikicin ya fara.

Mawallafi: Abdurrahman Hassane

Edita: Usman Shehu Usman